11 Mayu 2025 - 21:00
Source: ABNA24
Falasdinawa 1,500 Sun Rasa Idanunsu A Hare-Haren Ta’addanci Da Isra’ila Ke Kaiwa Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a yau Lahadi cewa, a sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza da ci gaba da mamaye yankin Gaza da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suke yi, Falasdinawa 1,500 ne suka rasa idanunsu.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbaiti (as) ya habarta cewa:   Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa: sakamakon hare-haren ta’addanci da gwamnatin sahyoniyawan ta ke yi a Gaza da kuma tsananin karancin magunguna, Palasdinawa kimanin 1,500 ne suka rasa idanunsu, yayin da wasu 4,000 kuma suke fuskanci irin wannan hatsari.

Wakilin Aljazeera ya kuma bayar da rahoton cewa: bayan harin da aka kai a yauLahadin da ta gabata a tantunan 'yan gudun hijira a garin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, mutane 9 ne suka yi shahada ciki har da yara 4.

Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta kuma bayar da rahoton a yau Lahadi cewa, tana da dubban manyan motoci da ke shirin shiga Gaza, kuma tawagoginta a shirye suke su fadada ayyukan raba kayan agaji.

Kungiyar ta kara da cewa: idan har ba a kawo karshen harin na Gaza da aka kwashe tsawon kwanaki 71 ana yi ba, to kuwa za a ci gaba da yin illa da wahalhalu ga fararen hula.

Bugu da kari, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayar da rahoton cewa, a cikin makon da ya gabata, wasu tsofaffin Falasdinawa 14 ne suka mutu sakamakon yunwa, rashin abinci mai gina jiki, da kuma rashin kula da lafiya, lamarin da ya kara tsananta sakamakon killace yankin.

Cibiyar kare hakkin bil adama ta Euro-Mediterranean ta bayar da rahoton cewa: Tsofaffi da yara kanana Falasdinu sannu a hankali suna mutuwa sakamakon munanan yanayin rayuwa da Isra'ila ke gallazawa masu da gangan.

Daga ranar 18 ga Maris, 2025 zuwa yanzu, adadin wadanda aka tabbatar a Gaza ya kai 2,710, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 7,432.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar, an kuma tabbatar da cewa: tun bayan fara hare-haren da gwamnatin Sahayoniya ta kai a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 (15 Mehr 1402), adadin shahidai ya kai 52,810, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 119,473.

Your Comment

You are replying to: .
captcha